Aƙalla mutane 5000 ake fargabar sun mutu a zanga-zangar Iran
17 January 2026

Aƙalla mutane 5000 ake fargabar sun mutu a zanga-zangar Iran

Mu Zagaya Duniya

About

Mahukuntan Iran sun yi barzanar amfani da hukuncin kisa kan masu zanga-zangar wadda ta juye zuwa tarzoma inda ofishin babban mai shigar da ƙara na gwamnati ya ce akwai yiwuwar idan aka fara ɗaukar wannan mataki a samu sassaucin zanga-zangar.

A nasa bangare shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar daukar mataki mai tsauri kan Iran muddun hukumomin ƙasar suka fara kashe masu  zanga-zangar tsadar rayuwa.