
About
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir a wannan makon ya mayar da hankali kan wasu daga cikin ɗabi’un jikin ɗan adam da kan faru ba tare da shiri ba, cikin waɗannan ɗabi’u kuwa har da hamma, inda shirin zai duba tasirinta ga lafiyar ɗan adam.
Rubuce-rubucen masana game da ɗabi’ar ta hamma na alaƙanta ta da barci ko gajiya ko kuma yunwa, sai dai fa masanan sun kuma bayyana cewa Hammar na taka muhimmiyar rawa a tsarin lumfashin ɗan adam, musamman ta fuskar daidaita yawan iskar da mutum ke shaƙa wato Oxygen da kuma wadda ya ke fitarwa wato Carbon dioxide.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.