Yadda yakamata jama'a su kula da cimakarsu a lokacin azumin Ramadan
23 February 2026

Yadda yakamata jama'a su kula da cimakarsu a lokacin azumin Ramadan

Lafiya Jari ce

About

Shirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako zai mayar da hankali kan cimaka a lokacin azumin watan Ramadana, dama yadda wasu ke fuskantar matsaloli masu alaƙa ɓacin ciki sakamakon yanayin ciye-ciyen da akan yi ko dai a lokacin buɗa baki ko kuma sahur.

Kamar yadda ya ke bisa al’ada a irin wannan lokaci na azumin watan Ramadan, musulmi kan ƙauracewa abinci da abin sha tun gabanin ketowar alfijir har zuwa  bayan faduwar rana, wanda hakan kan jefa masu azumin cikin yanayi na yunwa da kishirwa, sai dai da zarar an buɗi baki mutane kan ci duk abin da suke shawa lamarin da a wasu lokuta kan haddasa ɓacin ciki.

A lokuta da dama masana kan gargaɗi jama’a game da cin duk abin da ransu yake so a lokacin da suka buɗi baki, da nufin baiwa lafiyarsu kariya daga cutuka ko lalacewar ciki, dangane da wannan muka nemi ji daga bakin ƙwararru a fannin abinci da amfaninsa a jikin dan-adam.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.