Illar ta'ammali da magungunan ƙara kuzari ko rage gajiya da jama'a ke yi
22 December 2025

Illar ta'ammali da magungunan ƙara kuzari ko rage gajiya da jama'a ke yi

Lafiya Jari ce

About

Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan karon ya mayar da hankali kan yadda ɗabi’ar ta’ammali da wasu nau’ikan tsumin gargajiya da sunan samun kuzari ko kuma ƙarfin jiki ke ci gaba da ta'azzara tsakanin jama'a, wanda masana suka yi ittifaƙin na da matuƙar illa ga lafiyar jama’a.

Tsumi na baya-bayan nan da ke samun karɓuwa tsakanin jama’a musamman masu ayyukan ƙarfi shi ne ‘’Wankin ciki’’ ko kuma Gyaran Gida ko kuma Aji Garau kamar yadda wasu ke kiranshi, tsumin da ke ɗauke da magungunan gargajiya, kuma ya ke ci gaba da samun karɓuwa tsakanin dukkanin rukunin mutane kama daga matasa da kuma magidanta.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.