Skip to content
Opens in a new window
Yawaitar ɓarkewar cutar Diptheria a sassan jihohin Najeriya
05 October 2026

Yawaitar ɓarkewar cutar Diptheria a sassan jihohin Najeriya

Lafiya Jari ce

About

A wannan makon shirin ya yi duba kan cutar Diptheria, ko kuma mashaƙo, cutar da a baya-bayan nan ake yawan ganin ɓarkewar annobarta a wasu sassa na jihohin Najeriya wadda kuma ke kisan ɗimbin mutane baya ga kwantar da dama a asibitoci, inda wasu alƙaluma ke cewa daga watan Janairu zuwa Agustan shekarar nan mutane dubu 16 da 997 suka kamu da cutar a sassan Najeriya.

Masana sun yi ittifaƙin cewar mashaƙo ko kuma Deptheria tafi shafar yaran da ba a yiwa rigakafin cutuka ba ƴan shekara 1 zuwa 14 kodayake a wasu lokutan akan samu hatta waɗanda aka yiwa rigakafin sun kamu.

Latsa alamar sauti don sauraren shirin...