Yadda tsananin zafin bana ke barazana ga lafiyar jama’a a Arewa
27 April 2026

Yadda tsananin zafin bana ke barazana ga lafiyar jama’a a Arewa

Lafiya Jari ce

About

A wannan makon, shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan tsananin zafin da ake fuskanta a wasu jihohi na yankin Arewacin Najeriya, wanda masana suka yi ittifaƙin ya kai matakin da ka iya haddasa wasu cutuka ko kuma tayar da kwantattu.

Zafin na bana ya sha bamban da wanda aka saba gani a kowace shekara, domin jama’a na bayyana cewa ya daɗe bai lafa ba kamar yadda aka saba gani a shekarun baya, sai dai ko waɗanne cutuka ne ke haɗari ɓulla ko kuma waɗanda ke iya tashi koma nau’ikan mutanen da ya kamata su yi tsaka-tsan-tsan da lafiyarsu? Tambaya kenan ga ƙwararren jami’in lafiya Abdullahi Isma’ila ƙwalwa.