
About
Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba ne kan cutar ɗan sanƙarau ko kuma meningitis, cutar da a yanzu haka wasu ƙasashe ke cikin haɗarin fuskantar ɓullarta musamman a yammacin Afrika, waɗanda dama ke a tubalin fuskantar wannan cuta lokaci zuwa lokaci.