19 October 2026
Tsadar maganin asibiti ya tilasta wa wasu jama'a komawa amfani da gargajiya
Lafiya Jari ce
About
A wannan makon shirin ya yi nazari kan yadda tsadar maganin asibiti ke tilastawa jama’a karkatawa amfani da magungunan gargajiya, kodayake akwai kiraye-kirayen masana game da illar waɗannan magunguna a mahangar likitanci.
A ƙasashe irin Najeriya magungunan na gargajiya na matsayin hanyoyin neman waraka wanda aka gada tun kaka-da-kakanni kuma aka yi amanna da tasirinsu, duk kuwa da kiraye-kirayen ƙaurace masa dama ƙorafe-ƙorafe kan illolinsa nan da can, musamman daga likitoci da sauran jami’an lafiya.