About
A wannan makon shirin zai yi duba ne kan matsalar Antimicrobial resistance, wato wani yanayi da ake kaiwa ta yadda ƙwayoyin cuta ke bijirewa magunguna a jikin ɗan adama, matsalar da ke ƙoƙarin zama ruwan dare a duniya, wadda kuma wasu alƙaluman hukumar lafiya ke cewa tana sabbaba asarar rayukan aƙalla mutum miliyan guda duk shekara.
Masana a ɓangaren na kiwon lafiya na ganin cewa akan kai gaɓar ta fuskantar Antimicrobial resistance ne sakamakon dalilai da dama ciki kuwa har da yawaita amfani da magunguna kashe ƙwayoyin cuta wato Antibiotics sai kuma rashin ingancin magunguna ko kuma shan su barkatai ba tare da sahalewar likitoci ba.