About
Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya yi duba ne kan cutar Ebola da yanzu haka ke barazana ga duniya musamman ƙasashen nahiyar Afrika tun bayan ɓullarta a Jamhuriyyar Congo cikin watan Mayun shekarar nan.
Kawo yanzu cutar ta Ebola nau’in Bundibugyo da ba a iya kai ga nasarar samar da magani ko kuma rigakafinta ba, ta kashe mutanen da yawansu ya haura dubu 5 cikin mutum fiye da dubu 10 da suka harbu a Congo, yayinda a ɓangare guda ta fantsama wasu ƙasashen Afrika.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu...........