Ƙalubalen da majinyata ke fustanka na yawan sauya magungunan da likitoci ke musu
Lafiya Jari ce
Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon yayi dubu ne kan yadda likitoci ko jami’an lafiya ke sauya magungunan da marasa lafiya suka siyu duk tsadarsu, ko da kuwa ba a kai ga kammala amfani da su ba, wani lamari da ke ciwa majinyata tuwo a ƙwarya.
A galibin asibitoci ko cibiyoyin lafiyar da ke Najeriya, ba sabon abu ba ne, Likita ya rubutawa maras lafiya magani wani likitan na daban ya sauya, ba tare da la’akari da kuɗin da aka kashe wajen sayen maganin ko kuma halin da iyalai ke shiga gabanin samun sukunin siya ba, lamarin da ke sanya tunanin ko akwai gasa a tsakanin jami’an na lafiya ko kuma rashin yadda da ƙwarewar wani ɓangare, wannan kuwa batu ne da ke janyo ƙorafe-ƙorafe tsakanin jama’a.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu...........