Skip to content
Opens in a new window
Illar da ke tattare da shan magani ba tare da shawara ko umarnin likitoci ba
07 September 2026

Illar da ke tattare da shan magani ba tare da shawara ko umarnin likitoci ba

Lafiya Jari ce

About

Shirin lafiya jari ce a wannan karon ya mayar da hankali kan ɗabi'ar shan magani ba tare da shawara ko umarnin likitoci ba, wanda a turance ake kira Self-medication da kuma illar hakan ga lafiyar jama’a.

Wasu alƙaluma sun nuna cewa fiye da kashi 70 cikin ɗari na ƴan Najeriya ne yanzu haka sun bijirewa ziyartar asibitoci ta yadda suke shan magungunan tarin cutuka ba tare da umarnin ƙwararru ba, musamman a ɓangaren cutukan da suka shafi zazzabin cizon sauro da ciwon kai da kuma tari baya ga ciwon gaɓoɓi ko ma ciwon ciki dama ciwon kunne ko ciwon haƙori da sauransu.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.............