Ra'ayoyin masu saurare akan sulhu da 'yan bindiga
16 September 2025

Ra'ayoyin masu saurare akan sulhu da 'yan bindiga

Labarai

About

A Najeriya, al’ummar Birnin Gwari a jihar Kaduna na ci gaba da murna saboda samun zaman lafiya yau kusan watanni 10, yayin da a can Katsina al’ummomi ke fatan samun hakan ta hanyar kulla yarjeniyoyin zaman lafiya tsakakinsu da ƴanbinda.

To sai dai bayanai daga jihar Zamfara na cewa ko a jiya litinin, ƴanbinda sun kai farmaki tare da kwashe dimbin masallata a wani ƙauye da ke yankin Tsafe, duk da cewa akwai yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin ɓangarorin biyu.

Shin ko me za ku ce a game da irin wannan sulhu?