About
Shirin a wannan mako tare da Ahmed Abba zai mayar da hankali ne kan yadda na’ura da aka ƙimsawa tunanin ɗan adam wato AI ke sauya harkokin banki a duniya.
Artificial Intelligence, wato fasahar AI, na ƙara sauya yadda ake gudanar da harkokin tattalin arziki a duniya, ciki har da bankuna da hada-hadar kuɗi.
Daga gano zamba cikin mu’amalolin kuɗi zuwa tantance masu neman rance, ba da amsoshi ga abokan ciniki da kuma sa ido kan hada-hadar kuɗi, fasahar AI na samar da sabbin hanyoyin gudanar da harkokin banki cikin sauri da inganci.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.