Har yanzu Malama tsangaya na amfani da Ajami wajen musayar sakonni
11 November 2025

Har yanzu Malama tsangaya na amfani da Ajami wajen musayar sakonni

Ilimi Hasken Rayuwa

About

Shirin a wannan mako, kareshe ne kan maudu’in da muka tattaunawa a makonni biyun da suka gabata, wanda ya mayar da hankali kan yadda rubutun Ajami a kasar Hausa ya yi shura, da kuma yadda yake neman bacewa a wannan zamani.

Yayin da ake ganin har yanzu a Jamhuriyar Nijar, akwai yankunan da suke amfani da ajami wajen isar da sakonni, Malaman tsangaya daga Najeriya ma suna amfani da wannan tsarin rubutu wajen musayar bayanai a tsakaninsu.

Yaɗuwar addinin Islama a Ƙasar Hausa masana suka ce, ya taimaka sosai wajen shaharar wannan salo na rubutu, sannan kuma ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen inganta hanyoyin sadarwa na wancan lokaci.

A tattaunawarmu da masanin tarihi daga Kanon Najeriya, farfesa Tijjani Naniya, ya bayyana cewa, zuwan turawan mulkin mallaka, shine musabbabin gushewar wannan rubutu a kasar Hausa, amma a wancan lokaci, rubutun na ajami ya ci kasuwa tsakanin masana, malamai, sarakuna da kuma ‘yan kasuwa.