Shirin kawar da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta na samun nasara a Jigawa
02 June 2026

Shirin kawar da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta na samun nasara a Jigawa

Ilimi Hasken Rayuwa

About

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan makon ya sake waiwayar matsalar nan ce ta yawaitar yaran da ba za zuwa makaranta a arewacin Najeriya, batun da a fannin ilimi ke ci wa al’ummar yankin tuwo a ƙwarya. 

Masu iya magana dai na cewa ‘mai rai ba ya rasa motsi’ domin kuwa duk da girman da wannan matsala ta yi a Najeriya musamman ma yankin arewacin ƙasar, akwai waɗanda suka tashi tsaye wajen ganin sun kawo ƙarshen wannan ƙalubale, kuma har ma an fara samun sakamako kyakkyawa.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman................