17 November 2026
Yadda ƙungiyoyi masu zaman kansu ke baiwa ilimi tallafi a arewacin Najeriya
Ilimi Hasken Rayuwa
About
Shirin wannan mako ya duba yadda ake cigaba da ƙoƙartawa ne wajen samar da tallafin karatu ta hannun ƙungiyoyi da kuma Gidauniyar da ake kafawa a wurare daban daban a yankin Arewacin Najeriya.
Ga misali a waccan makon da ya gabata, gidauniyar Muktariyya da ke jihar Kano ta yaye ɗalibai kusan dubu 2000, waɗanda aka ilimantar a fannonin na’ura mai ƙwaƙalwa da kuma aikin Jarida bayan da suka kammala ɗaukar horon neman ƙwarewa kyauta tsawon shekara guda.
Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.