
Makarantu a Kano sun fara kai ƙarar iyayen yara sabida bashin kuɗin makaranta
Ilimi Hasken Rayuwa
Shirin ilimi Hasken rayuwa na wannan mako dubi ne kan yadda makarantu masu zaman kan a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, suka fara ɗaukar matakin kai ƙarar iyayen yara gaban hukumomi, sakamakon rashin biyansu kuɗaɗen karatun ƴaƴansu na tsawon lokaci.
Abin damuwar shine, idan iyayen suka tara kuɗin makaranta har ya kai matakin da ba za su iya biya ba, sai su sauya wa yaran nasu wurin makarantu, kenan wancan kuɗi da ake binsu ya bi ruwa.
Babbar matsalar ita ce, wannan al’amari a wasu lokutan ya kan haifar da ƙalubale ga ɓangarorin da ke gudanar da irin wadannan makarantu, abin da har ke kaiwa ga rufewa ko kuma sayar da makaranta, saboda rashin isassun kuɗin da za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna..........