Yadda Sunayen Zamani Suke Neman Kawar Da Na Hausawa
08 April 2026

Yadda Sunayen Zamani Suke Neman Kawar Da Na Hausawa

Daga Laraba

About

A tsakanin Hausawa, sunaye masu alaka da harshen Larabci sun kusan maye gurbin na  gargajiya irin su Tanko da Talle da Audi da dai sauran su.
 
 

Sai dai yayin da a da sunayen da Hausawa kan sanya wa  ’ya’yansu na Annabawa ko Sahabbai ko mashahuran malaman Muslunci ne, a baya-bayan nan wasu iyaye kan aro wasu kalmomi su rika kiran ’ya’yansu da su.

Mene ne dalilin hakan, yaushe kuma daga ina ya samo asali, kuma mene ne tasirinsa a al’adance da ma a addinance?
 
 

Amsoshin wadannan da ma wasu tambayoyi makamantansu shirin Daga Laraba na wannan makon zai binciko