
21 January 2026
Shin Ko Dawowar Dimokradiyya Ta Samar Da Kyakkyawan Fata Ga ‘Yan Najeriya?
Daga Laraba
About
A farkon Jamhuriya ta Hudu a shekarar 1999, dawowar Najeriya mulkin dimokuraɗiyya ya haifar da babban fata a zukatan ‘yan ƙasa, inda mutane suka yi tsammanin ƙarshen mulkin soja zai kawo adalci, ci gaban tattalin arziƙi, tsaro, da shugabanci nagari da ke sauraron muradin jama’a.
Jama’a sun yi imanin cewa za su sami ‘yancin faɗar albarkacin baki, ingantaccen zaɓe, aikin yi, da rage talauci ta hanyar shugabannin da suka fito daga zaɓin jama’a.
A cigaba da kawo muku shirye-shirye gabanin muhawarar Daily Trust shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi waiwaye ne don jin irin fatan da ‘yan Najeriya ke da su bayan dawowar Demokradiyya.