
About
A zantawarsa da Radio France Internationale, da France 24 da kuma TV5 Monde a ƙarshen taron Afrika da Faransa da aka kammala birnin Nairobi na ƙasar Kenya, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana matsayinsa a game da taɓarɓarewar sha’anin tsaro a Mali da kuma alaƙar Faransa da sauran ƙasashen Afirka ta fannin tsaro da aikin soji.
To amma da farko shugaban ya fara amsa wata tambaya ce dangane da dalilan da suka sa Faransa ke ci gaba da taka rawa a wajen tafiyar da takardar kuɗin CFA. Ga dai tattaunawar.
Latsa alamar sauti domin sauraren zanatawar.