
About
Ɗan takarar ƙawancen jam’iyyun da ke mara wa gwamnati baya a Jamhuriyar Benin ya yi nasarar lashe 94% na ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen shugabancin ƙasar da aka hana fitattun ƴan adawa tsayawa takara.
Romuald Wadagni mai shekaru 49 a duniya, shi ne ministan kuɗi tsawon shekaru 10 kafin shugaba mai barin gado Patrice Talon ya gabatar da shi a matsayin wanda yake son gaje shi.
Don jin yadda masu sharhi kan siyasar ƙasa da ƙasa musamman a Nahiyar Afrika ke kallon zaɓen na Jamhuriyar Benin, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Janjouna Ali Mahamane Sani.