Yadda gwamnatin Katsina ta gudanar da taron masu zuba jari a Faransa
17 April 2026

Yadda gwamnatin Katsina ta gudanar da taron masu zuba jari a Faransa

Bakonmu a Yau

About

A ƙoƙarinta na ganin ta bunƙasa harkokin tattalin arzikinta, gwamnatin jihar Katsina ta ce ƙofofinta a buɗe suke ga masu  zuba jari na ƙasashen ƙetare.

A yayin wani taro na masu zuba jari da ya gudana a birnin Paris na Faransa, gwamnatin jihar Katsina ta ce akwai masu zuba jarin da suka nuna sha’awar zuba jari a ɓangaren noma da ma’adinai da kiwon lafiya a jihar.

Domin jin irin matakan da suke ɗauka domin cimma wannan narasa, Khamis Saleh ya tattauna da mataimakin gwamnan jihar Kastina Malam Faruk Lawal Jobe.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.