About
An gaza cimma matsaya a taron Sauyin Yanayi na COP31 da aka ƙarƙare ranar Lahadi a Turkiya, bayan da ƙasashe da dama, ciki har da na Ƙungiyar Tarayyar EU, suka yi watsi da ƙudurin da aka gabatar, saboda ƙin jaddada illolin nau’ikan makamashi masu gurɓata yanayi na fetur da gas da kuma Kwal.
Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Umar Saleh Anka, babban Daraktan kula da Sauyin Yanayi na ma’aikatar Muhalli ta jihar Kano, wanda ya halarci taron na COP31.