
About
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada aniyar sa ta samar da Yan Sandan jihohi domin samar da tsaro. Tinubu ya bayyana haka ne yayin ganawa da masu ruwa da tsaki na jihar Filato mai fama da tashin hankalin.
Alhaji Isa Tafida Mafindi, wanda ya wallafa littafi a kan samar da Yan Sandan jihohi ya mana tsokaci a kai, yayin tattaunawar su da Bashir Ibrahim Idris.
Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...