Opens in a new window
Tattaunawa kan matsalar hare-haren ƴanbindiga a makarantun Najeriya
16 July 2026

Tattaunawa kan matsalar hare-haren ƴanbindiga a makarantun Najeriya

Bakonmu a Yau

About

Matsalar tsaro ta hare-haren da ‘yan ta’adda kan kai wa makarantu ko ɗalibai a sassan Najeriya, na ci gaba da ci wa  al’ummar ƙasar tuwo a ƙwarya, la’akari da cewar ko a baya bayan nan, ‘yan bindiga sun kai hari tare da sace wasu ɗaliban wata Sakandare a ƙaramar hukumar Dekina da ke jihar Kogi.

Wannan ya zo ne bayan hare-haren da a makwannin baya makarantun suka fuskanta a jihohin Oyo da kuma Borno.

Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da shugaban ƙungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya, Comrade Audu Titus Amba.

Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.