Tattaunawa da shugaban ƴan kasuwar arewa a Imo kan janye dokar tilasta zaman gida
09 February 2026

Tattaunawa da shugaban ƴan kasuwar arewa a Imo kan janye dokar tilasta zaman gida

Bakonmu a Yau

About

Kungiyar IPOB da ke fafutukar neman ɓallewar Yankin Kudu Maso Gabashin ƙasar daga Najeriya, ta sanar da kawo ƙarshen tilasta wa jama’a zaman gida a kowace ranar litinin yau kusan shekaru biyar kenan.

Matakin dakatar da tilasta zama gidan da ƙungiyar ta sanar a jiya lahadi, ya zo ne bayan da gwamnan jihar Anambra ya buƙaci jama’a su bijire sannan su ci gaba fita kowace litinin domin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Alhaji Ibrahim Abdulƙadir Ɗan-Ghali shi ne jagoran ƙawancen ƙungiyoyin ƴankasuwa ƴan asalin Arewacin Najeriya mazauna jihar Imo, ya bayyana wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal matsayinsu game da sanarwar ta IPOB.

Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.