
13 July 2026
Tattaunawa da Ibrahim Garba Wala kan matsalar tsaro da sace ɗalibai a Najeriya
Bakonmu a Yau
About
Yayin da ake ci gaba da jinjina wa rundunar sojin Najeriya saboda nasarar ceto ɗalibai da malamai 44 da ƴanbindiga suka yi garkuwa da su a jihar Oyo, wasu na gani cewa ya kamata mahukunta su ƙara azama don ceto ɗaruruwan mutanen da ake ci gaba da yin garkuwa da su a sasan ƙasar.
Ko a jiya lahadi ɗimbin mutane ne suka gudanar da zanga-zangar neman gaggauta ceto ɗalibai da dama da ake yin garkuwa da su a jihar Borno ciki har da waɗanda aka sace rana ɗaya da na jihar Oyo.
Abdoulkarim Ibrahinm Shikal ya zanta da Ibrahim Garba Wala da ke bin diddigin wannan batu na taɓarɓarewar tsaro a Najeriya, ga kuma zantawarsu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....