
About
Wasu fitattun mutane a Najeriya, da suka haɗa da tsohon shugaban hukumar zaɓe Farfesa Attahiru Jega, da tsohon jakadan ƙasar a Majalisar Dinkin Duniya Farfesa Ibrahim Gambari, sun yi gargaɗi a game da irin barazanar da ƙasar ke fuskanta sakamakon rashin tsaro, da yadda ake yi wa tsarin gudanar da zaɓuka na ƙasar karen-tsaye.
Kan wannan na gana da guda daga cikin masu ruwa da tsakin da suka yi wannan jan hankali, wato Hussaini Abdu na ƙungiyar Action Aid.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawar.