
07 January 2026
Tattaunawa da Dr Yahuza Getso kan ƙawancen tsaro tsakanin Najeriya da Amurka
Bakonmu a Yau
About
Masana da sauran jama’a gama gari a Najeriya, na ci gaba da ɗiga ayar tambaya kan makomar yarjejeniyar tsaron da aka sabunta tsakanin gwamnatin ƙasar da kuma Amurka, la’akari da cewar har yanzu babu wani cikakken bayani kan farmakin farko da Amurkan ta jagoranci kai wa ƴan ta’adda a jihar Sokoto.
Domin jin yadda ƙwararru kan fannin tsaro ke kallon lamarin, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Yahuza Ahmed Getso da ke Najeriya.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiayr hirar.