Tattaunawa da Dr Ruƙayya Yusuf Aliyu kan gargaɗin NBC ga kafofin yaɗa labarai
21 April 2026

Tattaunawa da Dr Ruƙayya Yusuf Aliyu kan gargaɗin NBC ga kafofin yaɗa labarai

Bakonmu a Yau

About

Hukumar Kula da kafafen Yaɗa Labarai a Najeriya NBC, ta gargaɗi masu gabatar da shirye-shirye a gidajen Radio da Talabijin da su guji bayyana ra’ayoyin ƙashin kansu, su kuma kaucewa yin katsalandan cikin bayanan waɗanda suka tattaunawa da su, da kuma yaɗa duk wani saƙo da ka iya haifar da rarrabuwar kai.

Tuni dai wannan mataki ya gamu da caccakar ƙungiyoyin farar hula da kuma ɓangaren ‘yan adawa a Najeriyar.

Kan haka, Nura Ado Suleiman ya tattauna Dakta Ruƙayya Yusuf Aliyu, Malama a tsangayar koyar da aikin Jarida na zamani a Jami’ar Bayero da ke Kano a Najeriya.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.