
26 March 2026
Tattaunawa da Dr Maman Kassou na jami’ar Andre Salifou a Nijar kan cinikin bayi
Bakonmu a Yau
About
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana fataucin bayi da aka share ɗaruruwan shekaru ana yi daga Afirka zuwa Turai da Amurka a matsayin ‘’cin zarafin bil Adama mafi girma’’ da aka taɓa gani a tarihi.
Ƙasashen duniya 123 ne suka kaɗa ƙuri’ar goyon bayan wannan ƙuduri, wasu uku wato Amurka, Isra’ila da Argentina suka ƙi amincewa yayin da wasu ƙasashe 52 suka yi ƙememe ta hanyar rowar ƙuri’unsu.
To domin tuni a game da lokacin da aka fara ɗibar bayi daga Afirka da kuma yadda hakan ya shafi ci gaban nahiryar, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da masani tarihi Dr Maman Kassou, malami a jami’ar Andre Salifou da ke Damagaram, ga kuma zantarwarsu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawar.