Tattaunawa da Dakta Ibrahim Adamu kan hare-haren Iran a ƙasashen Gulf
02 March 2026

Tattaunawa da Dakta Ibrahim Adamu kan hare-haren Iran a ƙasashen Gulf

Bakonmu a Yau

About

Iran ta kai jerin hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da wasu muhimman wurare biranen Dubai da Abu Dhabi a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sai kuma Doha a Qatar da kuma Manama a Baharain, domin ɗaukar fansa kan farmakin da haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar kanta tun daga ranar Asabar.

Baya ga harba makamai masu linzami kan Isra’ila, Iran ta tsananta kai hare-haren kan sansanonin sojin Amurka ne bayan mutuwar jagoranta Ayatollah Khamenei.

Domin jin halin da ake ciki da sauran batutuwa masu alaƙa da yaƙin da ya ɓarke, Nura Ado Suleiman ya tattauna Dakta Ibrahim Adamu, masanin Yankin Gabas ta Tsakiya da ke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawar.