Tattaunawa da Dakta Bashir Nuhu Mabai kan sake ta'azzarar yaƙin Iran da Amurka
05 March 2026

Tattaunawa da Dakta Bashir Nuhu Mabai kan sake ta'azzarar yaƙin Iran da Amurka

Bakonmu a Yau

About

Masana siyasar Duniya gami da rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya, na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan yaƙin da ya shiga rana ta shida tsakanin Iran da Amurka, wadda ke taimaka wa Isra’ila.

Ya zuwa jiya Laraba dai Isra’ilar ta yi iƙirarin kai wa Iran hare-hare sama da dubu 5, yayin da ita ma Amurka ke ci gaba kai wa Iran ɗin farmaki ta sama, da zummar rusa duk wani ƙarfi da ya rage wa gwamnatin ƙasar.

Kan wannan, da kuma yadda yaƙin ke daɗa rincaɓewa da shafar ƙasashen Yankin Gabas ta Tsakiya, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Bashir Nuhu Mabai, Malami a Jami’ar Dutsinma da ke Katsina a Najeriya.

Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar.