
23 February 2026
Tattaunawa da Aminu Bala Sokoto kan ta'azarrar hare-haren ƴanbindiga a Zamfara da Kebbi
Bakonmu a Yau
About
A Najeriya, ƴan bindiga a ƴan kwanakin nan sun zafafa kai hare-hare yankunan jihohin Zamfara da kuma Kebbi.
Na baya bayan nan shine wanda ya faru a garin Dutsen Dan Ajiya na karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara, inda rahotanni suka ce sama da mutane 30 sun mutu, bayaga na Tungan Dutse da mutane 50 suka rasa ransu.
Haka zalika, mayaƙan Lakurawa sun ƙara zafafa kai hare-hare a wasu sassa na jihar Kebbi, inda nan ma suka hallaka mutane da dama.
Kan haka Khamis Saleh na zanta da Squadron Leader Aminu Bala Sokoto.
Ku latsa alamar sauti don sauran cikakkiyar tattaunawar.