Tattaunawa da Alhaji Sani Shekarau kan buɗe iyakokin Najeriya da Nijar da Benin
11 February 2026

Tattaunawa da Alhaji Sani Shekarau kan buɗe iyakokin Najeriya da Nijar da Benin

Bakonmu a Yau

About

A ranar Litinin da ta gabata, mahukuntan Najeriya suka buɗe iyakokinsu da Nijar da kuma Jamhuriyar Benin ta ɓangaren jihar Kebbi, matakin da ya maido da zirga-zirgar kasuwanci tsakanin ƙasashen uku.

Gabanin buɗe iyakokin dai sai da aka gana tsakanin wakilan Najeriya da na Nijar,  matakin da ya kawo ƙarshen katse jigilar manyan motocin dakon kaya fiye da Dubu Ɗaya da Ɗari Biyar, da suka shafe aƙalla wata guda a tsaye.

Domin jin ƙarin bayani kan lamarin Nura Ado Suleiman ya tattauna da Alhaji Sani Shekarau, shugaban ƙungiyar manyan ‘yan kasuwa da ke jigilar kayayyaki zuwa ciki da wajen Jamhuriyar Nijar.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.