Tattaunawa da Alhaji Ouba Danlami game da babban zaɓen Kamaru
06 October 2025

Tattaunawa da Alhaji Ouba Danlami game da babban zaɓen Kamaru

Bakonmu a Yau

About

A Kamaru ana ci gaba da yaƙin neman zaɓen shugabancin ƙasar wanda za a gudanar ranar lahadi mai zuwa 12 ga wannan wata na Oktoba, inda ƴantakara 10 ke shirin fafatawa ciki har da shugaba mai-ci Paul Biya.

Akwai dai waɗanda suka janye daga zaɓen don mara wa wasu ƴantakarar duk da cewa an tantance su, yayin da wasu suka yanke shawarar mara wa wasu ƴantakarar haka kawai saboda wasu dalilai.

Alhaji Ouba Danlami, ya sha tsayawa takarar shugabancin  ƙasar a zaɓukan da suka gabata, to amma ban da wannan karo, ko saboda? Ga ƙarin bayanin da ya yi wa Ahmed Abba.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar..