
About
Yau ake cika shekaru biyu cif da ƙazamin harin da Mayaƙan Hamas suka kai Isra'ila wanya ya hallaka Yahudawa fiye da dubu guda sanadiyyarsa ne kuma aka faro wannan yaƙi na Gaza da ya kashe Falasɗinawa fiye da dubu 60.
Wannan yaƙi shi ne mafi muni da duniya ta gani a wannan ƙarnin wanda ya rushe fiye da kashi 90 na gine-ginen yankin.
Dangane da wannan ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin siyasar ƙasashe don jin tasirin wannan yaƙi ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar...