
About
Al’ummar yankunan ƙananan hukumomin Faskari da Ɗandume da ke jihar Katsina, na ƙoƙawa kan yadda ƴan ta’adda ke amfani da ranakun kasuwa wajen tare hanyar da ta tashi daga Ɗandume ta wuce zuwa Kadisau ta dangane da Sheme, inda su ke kwace musu ababen hawa da garkuwa da mutane harma a wasu lokuta da salwantar da rayukansu.
Haka nan a wasu lokuta ƴan ta’addan na kuma bin manoma gonakinsu don kwace musu babura da kuma shanun huɗa.
Khamis Saleh ya zanta da ɗaya daga cikin mazauna wannan yankin da wannan matsala ta daɗe tana ci musu tuwo a ƙwarya.