
About
Kwamitin da Sufeto Janar na Ƴansandan Najeriya Tunji Disu ya kafa domin bada shawarar yadda za’a kirkiro ƴansandan jihohi ya gabatar da shawarwarinsa ga kwamitin Majalisar tarayya dake yiwa kundin tsarin mulki kwaskwarima.
Shugaban kwamitin Farfesa Olu Ogunsakin ya bayyana cewar sun bada shawarar mayar da kashi 60 na ƴansandan tarayya da ake da su yanzu zuwa sabuwar rundunar ƴansandan jihohin da za’a kirkiro a jihohi 36 da Abuja.
Danna alamar sauti domin sauraron cikakkiyar hirar Bashir Ibrahim Idriss da Sufet Muhammed Wakili mai riyata....