About
Hausawa a ƙasar Togo kamar dai a sauran ƙasashe, sun gudanar da bukukuwan ranar Hausa ta duniya, inda suka yi amfani da wannan damar don tattauna al’adu da kuma tasirin wannan al’umma a cikin wannan ƙasar da ke Yamancin Afirka.
Abdoulaye Issa ya zanta da Souleyman Yahaya, shugaban cibiyar yaɗa al’adu da kuma kare muradun Hausawa a Togo, wanda ya yi masa ƙarin bayani a game da yanayin zamantakewarsu a ƙasar. Ga kuma tattaunawarsu.
Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...