About
Yau liitinin an shiga rana ta biyu kuma ta ƙarshe a ci gaba da taron ƙungiyar Francophonie da ta ƙunshi ƙasashe fiye da 90 masu mu’amala da harshen Faransanci a duniya, taron da ke gudana a birnin Phnom Penh na ƙasar Cambodia. Sai dai taron na wannan karo ya zo ne a cikin wani yanayi na taƙaddamar neman shugabancin ƙungiyar tsakanin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo da kuma Rwanda.
A game da wannan taro da kuma sauran ƙalubalen da ke gaban wannan ƙungiya, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Manazarci Sani Yahaya Janjouna.
Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu............