Sanata Abubakar Kyari kan makomar noma a Najeriya
13 May 2026

Sanata Abubakar Kyari kan makomar noma a Najeriya

Bakonmu a Yau

About

A ranar Talata ne ake kammala taron shugabannin ƙasashen Afirka da Faransa da ya gudana a birnin Nairobi ta ƙasar Kenya, wanda ya mayar da hankali kan hanyoyin ci gaban tattalin arziki da noma da samar da abinci ga jama'ar nahiyar.

Yaƙin Iran na ɗaya daga cikin abubuwan da ake ganin na maida hannun agogo baya wajen  magance ƙarancin abinci, musamman rufe mahsigin Hormuz da ake amfani da ita wajen safarar takin zamani.

Kan haka ne Nura Ado Suleiman ya zanta da ministan noman Najeriya Sanata Abubakar Kyari a wurin wannan taro, inda kuma ya ce su na ƙoƙarin magance matsalar.

Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.