About
A Najeriya masana da wasu ƴan ƙasar na ci gaba da ɗiga ayar tambaya kan rahoton cibiyar binciken tsaro ta SBM Intelligence, da ya nuna cewar ƴan ta’adda sun karɓi kuɗaɗen fansar da yawansu ya kai Dala miliyan 5.8, daidai da kusan naira biliyan 8 cikin shekara guda.
Rahoton, ya ce ƴan ta’addan sun ƙarbi kuɗaɗen ne a tsakanin watan Yulin shekarar bara ta 2025, da kuma Yunin bana, kuma mayaƙan Boko Haram ne suka amshe kaso 90 cikin 100 na jimillar kuɗaɗen.
Don jin yadda masana tsaro ke kallon wannan batu, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Muhd Sani Ibrahim Makiga.
Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...