
About
A daidai lokacin da ake kan tattaunawa tsakanin Iran da Amurka don samar da yarjejeniyar kawo ƙarshen yakin da ake yi tsakaninsu, kafafen yaɗa labaran Iran sun ce akwai gagarumin cigaba a tattaunawar.
Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Malam Mubarak Abdul-Aziz, ɗan Najeriya mazauni Tehran, wanda ya yi masa ƙarin bayani a game da halin da jama’a ke ciki daidai wannan lokaci da ake dakon cimma yarjejeniya don kawo ƙarshen wannan yaƙi.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.