
About
Nijar da Jamhuriyar Benin sun amince da yin aiki a tare don yaƙi da ta’addanci da ke addabar ƙasashen biyu na Yammacin Afirka, yayin da a hannu ɗaya suka kafa wani kwamitin da zai bayar da shawarwari cikin kwanaki 15 a game da yadda za a sake buɗe iyakokin ƙasashen da ke rufe yau kusan shekaru uku.
An dai cimma wannan matsaya ce a ziyarar da shugaban Benin Romuald Wadagni ya kai a birnin Yamai ranar talata, inda ya gana da takwaransa na Nijar Janar Abdourahman Tiani.
Shiga alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar da Abdulkarim Ibrahim Chikal ya yi da Sani Yahaya Djandjouna masanin siyasa ƙasa da ƙasa....