
27 January 2026
Masanin tsaro Muhammad Sani Ibrahim Makiga kan yunƙurin juyin mulki a Najeriya
Bakonmu a Yau
About
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da yunkurin yi wa shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu juyin mulki a watan Oktoban shekarar bara, lamarin da ya kai ga cafke wasu jami’an soji da ake zargin da hannunsu a yunƙurin.
A jiya Litinin ne dai Hedikwatar tsaron Najeriya ta hannun kakakinta Manjo Janar Sama’ila Uba ta tabbatar da lamarin, tare da sanar da miƙa rahoton bincikenta ga shugaban Najeriya.
Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da masanin tsaro a Najeriya Muhd Sani Ibrahim Makiga.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.