Mammane Wada kan shirin Nijar na kafa ƙungiyoyin samar da tsaro da basu makamai
01 April 2026

Mammane Wada kan shirin Nijar na kafa ƙungiyoyin samar da tsaro da basu makamai

Bakonmu a Yau

About

A Jamhuriyar Nijar, ra’ayoyi sun banbanta a kan shawarar da gwamnatin ƙasar ta yanke na kafa ƙungiyoyi waɗanda za ta bai wa horo tare da riƙe makamai don kare garuruwa daga hare-haren Ƴanbindiga.

A cewar gwamnati, jami’an ƙungiyoyin kare kan, za su kasance sojoji, da ƴansanda da sauran jami’an tsaron da suka yi ritaya, waɗanda za a riƙa biyansu kuɗin alawus.

Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Mammane Wada na ƙungiyar Transparency International da ke bibiyar lamurra a ƙasar ta Nijar.

Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu............