Kyaftin Bakoji kan ƙaruwar ayyukan ta'addanci a iyakar Najeriya da Nijar da Benin
27 February 2026

Kyaftin Bakoji kan ƙaruwar ayyukan ta'addanci a iyakar Najeriya da Nijar da Benin

Bakonmu a Yau

About

Wani rahoton bincike da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa, ya bayyana cewa an hare-haren ta’addanci a yankunan da ke iyakokin ƙasashen Najeriya, Benin, da kuma jamhuriyar Nijar sun ƙaru da aƙalla kaso 86 bisa 100, sakamakon yunƙurin da ‘yan ta’addan masu alaƙa da Al-Qa’eeda da IS ke yi na karɓe iko da hanyoyin da ratsa yankunan.

Rahoton ya ƙara da cewar matsalar wadda ta yi ƙamari a tsakanin shekarar 2024 zuwa bara, ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutane dubu 1000.

Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Kaftin Abdullahi Adamu Bakoji mai ritaya, masanin tsaro a Najeriya.

Latsa alamar sauti domin sauraren tataunawarsu...