30 September 2026
Ko janyewar dakarun Amurka sama da 4,000 a ƙasar Iraƙi nasara ce ga Iran?
Bakonmu a Yau
About
Amurka ta sanar da shirin janye sojojinta daga sansanoninsu na ƙarshe a Iraƙi zuwa ranar Laraba, matakin da Iran da ƙawayenta ke ɗauka a matsayin wata nasara, a ƙasar da sojojin Amurka 4,500 suka mutu cikin sama da shekaru 20 na yaƙi.
Ana ganin wannan a matsayin wata nasara ga ƙasar Iraƙi da ƙawayenta, ganin yadda ficewar sojojin Amurkan ke cikin sharuddan da Iran ta gindaya kafin dakatar da yakinta da Amurka, yayin da wasu ke ganin ko dai Amurka ta fara miƙa wuya a wannan yaƙi.
Game da wannan Rukayya Abba Kabara ta tattauna da Dakta Ibrahim Adamu masanin siyasar Gabas ta tsakiya, ga kuma yadda tattaunawar tasu ta kasance.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.